8 Satumba 2021 - 13:36
Libiya : MDD, Ta Yaba Da Sakin Saadi Gaddafi

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar Libya (UNSMIL), ta yaba da matakin da hukumomin kasar Libya suka dauka na sakin Al-Saadi Gaddafi, dan marigayi tsohon shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi wanda aka kifar da gwamnatinsa a shekarar 2011, tare da jami’an tsohuwar gwamnatin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tawagar ta bayyana sakin mutanen a matsayin muhimmin matakin mutunta dokoki da kare hakkin bil Adama, kuma wani babban cigaba ne wanda zai taimaka wajen bada gudummawa don cimma nasarar shirin warware rikicin kasar da kuma kara karfafa hadin kan al’ummun kasar.

A ranar Litini ne aka bayar da rahoton sakin Saadi Gaddafi da ake tsare da shi a gidan yarin Tripoli babban birnn kasar.

Tun a shekara ta 2014 ake tsare da Saadi Gaddafi wanda shi ne kwamandan runduna ta musamman a gwamnatin mahaifinsa, ya kuma tsere daga Libyane bayan kifar da gwamnatin mahaifinsa.

Gwamnatin hadaka ta Libiyar ta yi fatan sakin shi zai taimaka wurin samun hadin kan bangarorin dake rikici a kasar.

342/