6 Satumba 2021 - 13:35
Kwamandan Tawagar AlJazeera Na Hashdush-Sha’abi Ya Yi Shahada

Kwamandan Shirin AlJazeera Na Hashdush-Sha’abi ya yi shahada a "Jurful Nasar" da ke yankin Al'uwaisat da ke arewacin Babil, Iraki.

Bi sa rahoton kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) - ABNA, "Ash Shahid Asif", kwamandan "Al-Jazeera" Hashdush-Sha’abi ya yi shahada a "Jurful Nasar" a " Yankin Al'uwaisat"da ke arewacin Babil a Iraq.

Asef ya yi shahada sakamakon bam da aka dasa sannan wasu abokan aikinsa guda biyu sun samu raunuka a runduna ta 47 ta Hashdush-Sha’abi.
Wasu majiyoyin Iraki sun kuma rubuta cewa shahidin shi ne mataimakin kwamandan runduna ta 47.

342/