Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Tun a ranar Talata da ta gabata ce shugaba Ra’isi ya fara rangadin a Lardin Khozestan da ke gudancin kasar, lardin da ya yi fama da matsalolin ruwan sha a ‘yan watanin da suka gabata, inda ya ji ta bakin mutane kai tsaye ba tare da wani shamaki ba.
Ra’isi ya gana da jami’an gwamnati na lardin, kamar yadda ya gana da wakilan al’umma, haka nan kuma ya gana da mutane a cikin gari da kasuwanni da wuraren ayyuka, inda yake jin matsalolin jama’a da kuma bukatunsu kai tsaye daga bakunansu, domin sanin abubuwan da zai fara mayar da hankali a kansu wajen yi wa al’umma aiki.
Tuni shugaba Ra’isi ya bayar da umarni kawo karshen matsalar ruwa da aka samua wanan yanki, inda yanzu haka aikin ya yi nisa, kuma tuni ruwa ya fara wadata a mafi yawan yankunan da suka yi fama da matsalar ruwa saboda kafewar madatsun ruwa, sakamakon karancin ruwan sama a yankin.
Baya ga lardin Khozestan kuma, shugaba Ra’isi ya kama hanya zuwa yankin Sistan da Baluchestan, wanda yanki ne da galibin mazauna cikinsa ahlu sunnah ne, kuma ya kai ziyara ne ta bazata a yankin, domin ganewa idanunsa yanayin mutanen yankin da kuma tattaunawa da su, da ku jin bukatunsu ga gwamnatinsa.
342/