Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Takardar wadda babban sakataren hukumar ta NCC Farfesa Umar Dambatta ya sanyawa hannu, an bukaci kamfanonin da su gaggauta daukar wannan mataki domin taimakawa jami’an tsaro na ganin an cimma nasara wajen kawo karshen matsalar tsaro da ake fuskanta a yankin.
Wadannan mataken suna zuwa ne A daidai lokacin da gwamnonin jihohin Kaduna, zamfara, Nigeria, Katsina, Niger suka fitar da sabbin dokoki da ya hada da rufe kasuwanni da sauransu a kokarin da suka yi na ganin an dakile hare-haren da yan bindigan dajin suke kaiwa a wadannan jihohi.
342/