Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : A lokacin da yake magana kan halin da ake ciki a Afganistan a taron majalisar ministocin kasar na jiya Laraba, shugaba Raisi ya ce, tarihi ya tabbatar sau da dama cewa, kasancewar Amurka a wasu kasashe da yankuna ba ya shayo kan lamuran tsaro, da kwanciyar hankali da zaman lafiya a duniya.
Ebrahim Raisi ya ce, abubuwan da suka faru a Afganistan a cikin shekaru 20 da suka gabata, wata alama ce dake bayyana hakikanin take hakkin dan Adam a wannan zamanin na yau.
Sannan idan aka duba yawan mata da yaran Afghanistan da aka kashe, ko kuma aka raunata a tsawon shekarun nan, za a iya gane cewa, bala’i yana faruwa a Afghanistan.
Kasancewar Amurka a kasashen waje bai taba haifar da tsaro ba, sai dai ya lalata shi, ya kuma wargaza kwanciyar hankali, da zaman lafiya, inji shugaban kasar ta Iran.
342/