1 Satumba 2021 - 11:58
An Fara Yunkurin Tashin Rukunin Farko Na Masu Ziyarar Arbaeen Zuwa Karbala

Kimanin wata guda ya rage ga Arbaeen Hussain, wasu Maziyartn Arbaeen din sun yi tattaki daga garuruwan Iraqi kamar Basra.

Bisa rahoton Kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) - ABNA , a duk shekara mutanen garuruwan Iraki suna tafiya zuwa Karbala da kafa daga nesa da kusa dan halartar Taron Arbaeen na Imam Hussain har zuwa ranar Arbaeen kuma tabbas kafin hakanan a wannan lokacin sun kasance a halarar Aljannar Ubangiji kuma sun samu damar Ziyarar Iyayan gidansu.

Ya zuwa Yanzu, wanda ya rage kusan wata guda ga Arbaeen din Hussain, wasu maziyartan Arbaeen din suna tattara jakunkunansu daga garuruwan Iraki suna tafiya zuwa Karbala da tutoci da aka yi wa ado da sunaye da lakubba na Imam Husaini (AS) da shahidan Karbala.

Daya daga cikin tawagogin maziyartan Arbaeen din da ke ziyartar Imam Husaini (AS) a kowace shekara suna samun halarta, maziyartan Birnin Basra wadanda su ke fara tafiya kimanin wata guda kafin Arbaeen Husain As don isa Karbala a cikin kwanakin Arbaeen.

Daga Basra zuwa Karbala Kimanin kilomita 520 ne maziyartan sun fara tafiya don isa haramin Imam Husaini (AS) a cikin kwanaki arba’in da suka gabata don share tafiyar sama da kilomita 500 a kafa tare da rakiyar sauran maziyartan.

A cewar kafar Labarai ta Fars, ranar Arbaeen zata zamo ita ce 5 ga watan Oktoba, ganin cewa gwamnatocin Iraki da Iran ba su yi wani takamaiman sharhi kan Arbaeen ba. maziyartan Iran suna jiran tafiya zuwa Arbaeen, tabbas hukumomin Iran sun yi wani shiri na yau da kullun don tura maziyartan, kuma la’akari da hanyoyin kiwon lafiya, kuma sanarwar tafiyar ya danganta da karɓar baƙuncin maziyarta daga wajen Iraki da hukamar Irakin zata sanar.

342/