Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a yayin ganawar da ta gudana tsakanin shugaban kasar Syria Bashar Assad da kuma ministan harkokin wajen Iran Amir Hossein Abdollahian, Assad ya jaddada matsayin kasarsa na ci gaba da yin aiki kafada da kafada tare da kasar Iran.
Assad ya ce kasashe biyu na Iran da Syria sun cimma nasarori masu tarin yawa, sakamakon yin aiki tare da juna a tsawon shekaru masu yawa, kamar yadda kuma ya jaddada cewa za su ci gaba da yin aiki tare a dukkanin bangarori, musamman ma a bangaren yaki da ta’addanci, da kuma harkokin tattalin arziki.
Wasu rahotanni sun ce ministan harkokin wajen kasar ta Iran ta isar wa shugaba Bashar Assad da bayani ne kan zaman taro da aka gudanar a birnin Bagadaza na kasar Iraki a ranar Asabar da ta gabata, dangane da muhimamncin yin aiki tare tsakanin kasashen yankin, da kuma lalubo hanyoyin warware matsalolinsu.
Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma gana da takwaransa na Syria Faisal Miqdad, kamar yadda ya gana da wakilan kungiyoyin Falastinawa da suke a birnin Damascus, inda ya jaddada musu aniyar Iran wajen ci gaba da taimaka ma Al’ummar Falastinu, duk kuwa da matsin lambar da take fuskanta sakamakon hakan.
342/