Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : a cikin wata sanarwa da suka fitar a yammacin jiya Lahadi, ‘yan awaren yankin Tigray na kasar Habasha sun zargi kungiyar Tarayyar Afirka da karkata ga manufofin gwamnatin dis Ababa.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar Tarayyar Afirka ke kokarin ganin ta shiga tsakani, domin sasanta ‘yan awaren na Tigray da kuma gwamnatin Habasha, bayan kwashe kusan shekara guda suna gwabza yaki, inad suke zargin cewa Tarayyar Afirka tana nuna karkata ga gwamatin Addis Ababa, wanda suke ganin da wuya a yi musu adalci.
Kungiyar Tarayyar Afirka dai ta nada tsohon shugaban Najeriya Alusegun Obasanjo a matsayin manzonta na musamman mai shiga tsakani a rikicin kasar ta Habasha, wanda zai tattauna da dukkanin bangarorin biyu, domin ganin an kawo karshen rikicin yankin Tigray.
Tun a cikin watan Nuwamban shekara ta 2020 da ta gabata ce aka fara gwabza fada tsakanin ‘yan tawayen yankin Tigray da ke arewacin kasar Habasha da kuma dakarun gwamnatin kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, tare da mayar da wasu fiye da miliyan biyu ‘yan gudun hijira.
342/