Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : ‘’bukatun shugaban Amurka Joe Biden, ba su da wani bambanci dana Donald Trump, wanda ya fice daga yarjejeniyar nukiliyar kasa da kasa ya kuma kakabawa Iran tsauraren takunkumai
Shugaban Amurka Joe Biden ya ce komawa cikin yarjejeniyar nukiliya Iran na daya daga cikin manyan manufofinsa na harkokin waje, amma ya ki daukar duk wani mataki na dawo da Washington a cikin yarjejeniyar.
Bayan shafe tattaunawa har sau shida tsakanin Iran da sauran wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliya a Vienna, gwamnatin Biden ta dora kan amfani da matsin lamba a yunkurin tankwaso Jamhuriyar Musulunci, inji Ayatollah Sayyid Ali Khamenei.
Jagoran ya bayyana hakan ne jiya Asabar yayin ganawa da mambobin sabuwar gwamnatin kasar.
A nasa bangare sabon shugaban kasar ta Iran, Ebrahim Ra’isi, ya bayyana cewa gwamnatins ana goyan bayan tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliyar, amma da sharadin tabbatar da muradun kasa.
Ya kuma jaddada cewa Iranba zata taba mika kai ga batun makamanta masu linzami da rawar da take takawa a yankin Gabas ta Tsakiya.
342/