29 Agusta 2021 - 10:22
​Iraki: An Bude Taron Kasa Da Kasa Dangane Da Tsaro A Gabas Ta Tsakiya

An bude taron kasa da kasa a birnin Bagdaza na kasar Iraki, da manufar tattauna matsalolin tsaro da fahintar juna tsakanin kasashen yankin Asia. Shuwagabanni da wakilai daga kasashen yankin da kuma wasu kasashe daban sun halarci taron.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : ya nakalto Husain Amir Abdullahiyan ministan harkokin wajen kasar Iran, a jawabinsa na farko a taron na Bagdaza yana cewa jumhuriyar Musulunci ta Iran tana maraba da dukkan shawarori masu amfani ga ci gaba da aiki tare a yankin kudancin Asiya da tekun farisa.

Ya kuma kara da cewa kasar Iran a shirye take ta bada gudumawarta wajen sake gina kasar Iraqi, bayan kubutarta daga hannun kungiyar Daesh yan shekarun da suka gabata.

Wannan dai shi taron farko wanda Amir Abdullahiyan yake halatta a kasashen waje a matsayinsa na ministan harkokin wajen kasar Iran.

Ana saran taron Bagdaza zai tattauna batutuwa da dama, wadanda suka hada da yakin yemen, matsalolin kasashen Syriya da Lebanon.

Sabon shugaban kasar Iran ya bayyana cewa kyautata dangantaka da kasashe makobta na daga cikin muhimman al-amuran da gwamnatinsa tasa a gaba.

342/