Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Saeed Khatibzadeh, ya yi tir da kakkausar murya da tagwayen hare -haren ta'addanci da aka kai a Kabul, ciki har da tashin bam a filin jirgin saman Kabul.
M. Khatibzadeh ya bayyana fatan cewa za a kafa gwamnati mai cikakken iko a Kabul cikin gajeren lokaci.
Haka kuma Iran ta yi fatan hukumomin da abin ya shafa zasu dauki nauyin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
342/