25 Agusta 2021 - 10:08
Afghanistan : Taliban Ta Bukaci Kasashen Yamma Su Rika Kwashe Baki Kawai

Kungiyar Taliban data kwace mulki a Afghanistan ta bukaci kasashen yamma dasu kwashe baki kawai daga kasar, ba wai su rika dibar kwararun ‘yan kasra ta Afghanistan suna fita dasu ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Da yake sanar da hakan kakakin kungiyar ta Taliban, Zabihullah Mujahid, ya ce ‘’ Amurkawa da kawayensu na dibar ‘yan Aghanistan kwararu da suka hada da injiniyoyi, don haka ya kamata a kawo karshen wannan’’.

Kungiyar ta kuma jadadda matsayinta na kin amincewa da fitar da mutane daga kasar ta filin jirgin saman Kabul bayan ranar 31 ga watan Agusta.

Kafin hakan dai mai ba da shawara kan harkokin tsaron Amurka, Jake Sullivan, ya ce Amurkar na tattaunawa da kungiyar Taliban yayin da wa’adin ranar 31 ga watan Agusta na janyewar dakarun kasar ke karatowa.

A ranar Litinin ne shugaban Amurka Joe Biden, ya bayyana yiwuwar tsawaita lokacin kammala kwashe mutane daga ranar 31 ga wata da Amurkar ta sanya domin kammala janye sojojinta daga Afghanistan.

342/