Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar Aljeriyan ta fitar bayan zaman majalisar ƙoli ta tsaron ƙasar ta ce ya zuwa yanzu an kama mutane 22 da suke da hannu cikin bala’in wutar dajin da ta faru wacce ta faro daga arewacin ƙasar sannan kuma ta yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 90 ciki kuwa har da sojoji 33 cikin mako guda.
Sanarwar ta ce asalin alhakin faruwar wutar daji yana wuyan ƙungiyar nan ce ta ‘yan adawa ta Rashad da kuma ta ‘yan aware ta MAK wacce take neman ‘yancin cin gashin kan yankin Kabylie.
Kafin nan dai hukumar tsaron ƙasar ta sanar da cewa binciken da ta gudanar ya nuna cewa akwai hannun ƙungiyoyin ta’addanci cikin wutar dajin kamar yadda ‘yan waɗannan ƙungiyoyin suka tabbatar bayan kama su da jami’an tsaro suka yi.
Har ila yau sanarwar ta ce a yayin zaman majalisar dai an tattauna batun alaƙar diplomasiyyar ƙasar da ƙasar Moroko wacce ta ke ci gaba da yin tsami sakamakon yadda Aljeriya take ci gaba da goyon bayan ‘yan ƙungiyar Polisario masu neman cin gashin kan yankin Sahara na ƙasar Moroko su kuma a na su ɓangare ƙasar Morokon tana goyon bayan ‘yan a waren yankin Kabylie.
342/