18 Agusta 2021 - 13:44
Uganda Za Ta Karbi ‘Yan Gudun Hijirar Aghanistan 2000

Hukumomi a Uganda sun ce kasar ta shirya saf domin karbar ‘yan Afghanistan dake gujewa rikici a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : Uganda ta ce za ta karbi ‘yan gudun hijirar na Afghanistan 2000 bisa bukatar Amurka.

Minista a gwamnatin Uganda, Esther Anyakun, ya ce rukunin farko na ‘yan Afghanistan 500 zai sauka a filin jirgin saman Entebbe, kuma za’a musu gwajin cutar korona da zarar sun sauka sanna a killace su.

Gwamnatin Amurka ce za ta kula da dukkan yaunin kula da su inji ministan.

Idan dai hakan ta kasance Uganda za ta zama wata kasa a nahiyar Afrika ta farko da ta karbi ‘yan gudun hijiran Aghanistan tun bayan da ‘yan Taliban suka kwace mulkin kasar.

Uganda dai ita ce kasa ta uku a duniya wajen karbar ‘yan gudun hijira.

342/