Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : Josep Borrell Babban jami’i mai kula da harkokin siyasar wajen kungiyar Tarayyar Turai ya ce, Taliban ta yi nasara a yakin kasar Afghanistan, saboda haka babu abin da ya rage ga kungiyar Tarayyar Turai sai bude kofar tattaunawa da ita.
Ya ce yin hakan zai taimaka wajen shawo kan matsaloli da za su iya faruwa, wadanda za su cutar da kasashen tarayyar turai, daga ciki kuwa har da kwararar ‘yan gudun hijira daga Afghanistan zuwa kasashen turai.
Baya ga haka kuma ya kara da cewa, za su ci gaba da kokarin kwashe jami’an diflomasiyya na kasashen turai gami da ‘yan kasar Afghanistan da suka taimaka musu daga kasar.
Borrell ya ce, tattaunawa da Taliban ba ya nufin amincewa da mulkinta ba ne, amma saboda maslaha ya zama wajibi a yi hakan, domin kuwa kasashen turai sun tafka babban kure, ta yadda suka yi zaton cewa dakarun Afghanistan za su iya maye gurbin dakarun kasashen turai idan suka fice daga kasar, wanda kuma hakan ne ya baiwa Taliban damar shimfida ikonta a kasar.
Sannan kuma ya jaddada cewa, dole ne filin sauka da tashin jiragen sama na birnin Kabul ya ci gaba da zama a bude, domin samun damar aiwatar da ayyukan kwashe sauran ‘yan kasashen turai da suka rage a kasar, kafin ganin abin da zai yi a nan gaba.
342/