ABNA24 : Wasu rahotannin sun ambato cewa sojojin Amurka sun bude wuta yayin da 'yan Afganistan ke kokarin shiga jiragen saman da ake korarin kwashe ‘yan waje.
Wasu bayanai na daban sun ce an samu mace mace yayin bude wutar da sojojin na Amurka sukayi koda wasu sun ce harbin sama ne akayi.
Amma kamfanin dilancin labaren Reuters ya ce mutane da dama sun mutu yayin rudanin.
342/