ABNA24 : Sanarwar da ke dauke da sa hannun jami'in yada labaran rundunar, CP Frank Mba ta ce DCP Disu zai kama aiki gadan-gadan ba tare da bata lokaci ba.
DCP Tunji Disu, zai maye gurbin Abba Kyari da aka dakatar kan zargin rashawa.
Hukumar kula da ayyukan 'yan sandan Najeriya ta dakatar da Abba Kyari, bayan da wani shahararren mai amfani da dandalin sada zumunta da ke fuskantar tuhumar aikata damfara a Amurka ya bayyana cewa su kan gudanar da wasu ayyuka tare.
Hukumar kula da harkokin ‘yan sanda a Najeriya ta ce wannan dakatarwar da aka wa Kyari za ta ci gaba da aiki har sai hukumar FBI ta Amurka ta kammala bincike.
A ranar Laraba, hukumar FBI ta Amurka ta ce Ramon Abbas ya yi damfarar kudi da ya kai dala miliyan 24 jimilla.
342/