29 Yuli 2021 - 14:52
An Sanar Da Ranar 5 Ga Watan Augusta A Matsayin Ranar Da Za’a Rantsar Da Sabon Shugaban Кasar Iran

Majalisar dokokin ƙasar Iran ta sanar da tsare-tsaren da aka tsara na rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Iran, Sayyid Ibrahim Ra’isi a gaban ‘yan majalisar kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.

ABNA24 : A wata sanarwa da majalisar ta fitar ta ce za a gudanar da bikin rantsuwa da kama aikin sabon shugaban na Iran ne a ranar Alhamis mai kamata wato 5 ga watan Augusta da misalin ƙarfe 5 na yamma agogon Iran wato 12:30 agogon GMT inda ake sa ran manyan baƙi na cikin gida da kuma na waje za su halarci bikin.

A ranar 18 ga watan Yunin da ya gabata ne dai al’ummar Iran suka zaɓi Sayyid Ibrahim Ra’isi a matsayin shugaban Iran na takwas bayan ya sami kimanin kashi 62 cikin ɗari na kuri’un da aka kaɗa, inda zai gaji shugaba mai ci Dr. Hasan Rouhani wanda wa’adin mulkinsa na biyu ya ke dab da ƙarewa.

A jiya ne dai shugaba Rouhani da ‘yan majalisar ministocinsa su ka kai ziyarar ban kwana ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, wanda ya jinjina musu kan irin ƙoƙarin da suka yi wajen ciyar da ƙasar ta Iran gaba da kuma kiran sabuwar gwamnatin da ta yi amfani da irin nasarorin da gwamnatin ta samu kamar yadda kuma ya yi ishara da wasu ɓangarori na gazawar gwamnatin wanda ya ce wajibi ne gwamnati mai zuwa ɗin ta ɗau darasi daga hakan musamman batun dogaro da ƙasashen yammaci.

342/