28 Yuli 2021 - 14:51
Iran Da Siriya Sun Karfafa Alakar Kasuwanci A Tsakaninsu

Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Na Ziyara A Siriya A wani Mataki Na Karfafa Huldar Kasuwanci

ABNA24 : A wani mataki na karfafa huldar kasuwanci tsakanin kasashen Iran da Siriya, shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya isa birnin Damascos, inda zai gana da manya jami’an Siriya da dama.

Mista Qalibaf, na tare da rakiyar wata babbar tawaga ta ‘yan majalisar dokokin Iran.

Ana sa ran zai gana da ‘yan kasuwa da masu zuba jari a kasar ta Siriya.

342/