Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Sojojin Yemen cikin kwanaki biyu da suka gabata a matsayin maida martani ga hare-haren sama na Saudiyya waɗanda suka kai ga shahada da raunata dubban fararen hular Yemen, sun gudanar da ayyukan soji masu faɗi da kai hari cikin ƙasar Saudiyya. Wannan aiki ya fara ne daga ranar da ta gabata da kai hari kan filayen jirgin sama na "King Khalid" a birnin "Riyadh" da "King Fahd" a birnin "Dammam" da wuraren kamfanin "Aramco" a yankuna da dama kuma ya ci gaba jiya kuma ya haɗa tun daga birnin Riyadh har zuwa birnin Jeddah da wasu biranen kudancin Saudiyya.
Bisa ga rahoton jaridar "Al-Akhbar" ta Lebanon, Saudiyya ma kamar lokutan da suka gabata a ƙarƙashin matsin lamba na hare-hare ta yi ƙoƙarin zargin Yemen da kai hari kan Makka Mai Girma da Madina Munawwara.
Zargin da Birgediya "Yahya Saree" mai magana da yawun sojojin Yemen, ya kwatanta da babbar ƙiren ƙarya. Ya nanata cewa waɗannan sojojin suna kai hari ne kawai kan wuraren Aramco da filayen jirgin sama na maƙiyin Saudiyya.
A cewar majiyoyin soji masu masaniya a birnin San'a waɗanda suka tattauna da jaridar "Al-Akhbar", aikin cikin kwanaki biyu da suka gabata bai tsaya ba kuma tun farkon tsanantar tashin hankali a ranar 20 ga Yuli da ya gabata, shine hari mafi faɗin aiki. Waɗannan majiyoyi sun ce sojojin Yemen kwanan nan sun shiga matakin aiwatar da manufar matsin lamba mafi girma.
Bisa ga sanarwar da aka wallafa, sojojin Yemen sun sanya filin jirgin sama na "King Khalid" a gaba a cikin maƙasudansu. Waɗannan sojojin a cikin wata sanarwa sun sake yi wa dukkan kamfanonin jiragen sama na ƙasa da ƙasa, ma'aikata da fasinjoji gargaɗi kan haɗarin amfani da wannan filin jirgin kuma sun nanata cewa aikin da ake kaiwa kan wadannan wurare zai ci gaba.
Wannan gargaɗin ya zo ne a daidai lokacin da hukumar kula da jiragen sama ta fararen hula ta Saudiyya ta bayyana cewa tana da niyyar sake fara ayyukan filin jirgin a hankali tun jiya. Hare-haren sojojin Yemen a farkon wannan watan sun riga sun haifar da rufe wannan filin jirgin.
Lalacewar Filayen Jirgin Sama Na Saudiyya Da Samun Matsalar Tashin Jirage
Majiyoyin soji a birnin San'a sun tabbatar wa jaridar "Al-Akhbar" cewa filin jirgin sama na "King Khalid" cikin kwanaki biyu da suka gabata an kai masa hari da manyan makamai masu linzami da yawa kuma waɗannan hare-haren sun yi mummunar barna ga sassansa daban-daban. A cewar waɗannan majiyoyi, aikin harin naci gaba da gudana ne da nufin lalata wasu filayen jirgin sama da hana su gudanar aiki.
A daidai wannan lokaci, masu fafutuka na Saudiyya sun bayyana cewa ayyukan filin jirgin sama na "King Fahd" a birnin Dammam tun sanyin safiyar jiya an dakatar da su sau da yawa. Shafukan yanar gizo na lura da zirga-zirgar jirage ma sun ba da labarin bayyanar matsaloli a ayyukan filin jirgin sama na "King Abdulaziz" a birnin Jeddah cikin ranar da ta gabata.
"Turki Al-Maliki" mai magana da yawun haɗin gwiwar Saudiyya, ya tabbatar da harin sojojin Yemen kan Riyadh da wasu yankuna na Saudiyya wanda ya faru da sanyin safiyar jiya, kuma ya ce nau’rorin kariyar sama sun kakkabo da wasu hare-haren.
Kamfanin dillancin labarai na Faransa ma ya ba da labarin faruwar gobara a wata cibiyar mai ta Saudiyya a birnin Riyadh kuma bisa ga majiyoyi ya ba da rahoton cewa tarin ginshiƙan hayaki sun tashi kusa da filin jirgin sama na "King Khalid."
Gargaɗin hukumar kare fararen hula ta Saudiyya ma suna nuni da cewa hare-haren makamai masu linzami na sojojin Yemen cikin ƙasar Saudiyya cikin kwanaki biyu da suka gabata suna ci gaba.
……………………..
Ra'ayinka