22 Yuli 2021 - 13:38
​‘Yan Sanda A Najeriya Sun Sami Nasara Kubutar Da Mutane 100 Wadanda ‘Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

Jami’an ‘yansanda a jihar Zamfara na tarayyar Najeriya sun bada sanarwar kubutar da mutane 100 wadanda ‘yan bindiga masu neman kudaden fansa suka yi garkuwa da su.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto kakakin ‘yansanda na jihar ta Zamfara Mohammad Shehu ya na fadara haka a yau Laraba, ya kuma kara da cewa ‘yan bindigan sun sace mutanen ne a ranar 8 ga watan Yunin da ya gabata a kauyen Manawa na jihar ta Zamfara.

Shehu ya kara da cewa ‘jami’ansa sun kubutar da mutanen ba tare da bada wani abu ba, kudi ko kaya. Sannan a halin yanzu za’a dubi lafiyarsu kafin a hadasu da iyalansu.

Rahotanni sun bayyana cewa a cikin watanni 6 na farko na wannan shekarar da muke ciki ‘yan bindiga sun sace mutane kimani 2,371 a duk fadin tarayyar Najeriya inda suke neman jimillar kudaden fansa na naira biliyon 10 wanda ya yi dai dai da dala miliyon 24.33. Sai dai ba’a san yawan kudaden da aka biyasu daga cikisa ba.

342/