ABNA24 : A wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar a ranar Lahadi, bangarorin sun ce za su sake haduwa da nufin hanzarta tattaunawar zaman lafiya bayan kwanaki biyu na tattaunawar da ba ta cimma gacci ba a birnin Doha, kamar yadda shafin gidan talabijin Al Jazeera ya rawaito.
Masu tattaunawar daga bangarorin da ke hamayya da juna, wadanda suka kasance a Doha tun ranar Asabar, sun ce "bangarorin biyu sun kuduri aniyar ci gaba da tattaunawa a wani babban mataki har sai an cimma matsaya".
Sanarwar ta kara da cewa "Za mu yi kokarin samar da kayayyakin jin kai a duk fadin Afghanistan."
Tsawon watanni kenan da bangarorin biyu ke haduwa a birnin Doha na kasar Qatar, ba tare da cimma wata nasara.
342/