ABNA24 : Mujallar ‘Women in Parliament’ ta kara da cewa banda kashi 61% na kujerun majalisar dokoki kasar ta Rwanda wanda mata suka samu, har’ila yau fiye da kashi 50% na majalisar ministocin kasar ta Rwanda mata ne.
Labarin ya kara da cewa banda kasar Rwanda kasashen Cuba da kuma Hadaddiyar daular larabawa ne suka zo matsayi na biyu da uku a jerin kasashen duniya wajen bawa mata mukamai na gwamnati da kuma kujeru a majalisun dokokin kasashe.
Daga karshe mujallar ta ce a wannan shekara ta 2021 kashi 25.5 % na mukaman gwamnatoci da kujeru a majalisun dokoki suna hannun mata, wanda ya nuna cewa an sami Karin kashi 0.6% a duniya gaba daya.
342/