11 Yuli 2021 - 12:22
​Saudiyya Ta Sanar Da Ranar Talatar Makon Gobe A Matsayin Ranar Idin Layya

Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da ranar ashirin ga watan Yulin da muke ciki a matsayin ranar idin babbar sallah.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da gwamnatin Saudiyya ta fitar, ta bayyana ranar sha tara ga Yulin da muke ciki a matsayin ranar Arafa, sannan kuma 20 ga watan Yuli a matsayin ranar idin babbar sallah ta wannan shekara.

Bayanin ya ce, sakamakon yadda aka duba jinjirin watan Zulhijjah a ranar jiya Juma'a amma ba a ga watan ba, a yau Asabar 29 ga watan Zulqaadah, ita ce ranar karshe ta wannan wata, gobe Lahadi tana a matsayin daya ga watan Zulhijjah.

Haka nan kuma hukumomin na Saudiyya sun bayyana cewa, a yau ma za a kara yin dubar jinjirin watan Zulhijjah, amma bisa ga lissafi yau Asabar yau ce ranar karshe ta watan Zulqaadah.

342/