10 Yuli 2021 - 13:06
Najeriya:‘Yan Bindiga Sun Kashe Akalla Mutane 45 A Karamar Hukumar Maradun Na A Jihar Zamfara

Yan bindiga sun kashe akalla mutane 45 a wani harin da suka kai a wasu kauyuka a karamar hukumar Marudn na jihar Zamfara.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa maharan kimani wadanda suka shigo yankin kan babura sun fara harbi kai mai uwa da wabi a kan mutane a cikinn kauyukan.

Rundnar ‘yansanda ta jihar ta tabbatar da aukuwar hakan ta kara kara da cewa abin ya auku ne a ranar Alhamis da misalign karfe 12 na rana, amma basu sami labarin ba sai jiya jumma’a.

Labarin ya kara da cewa kauyuwa da abin ya shafa dai sun hada da Gidan Adamu, Gidan Maidaji, Bauci, Wari, Kyara da kuma Gidan Maidawa.

342/