9 Yuli 2021 - 13:53
Dakarun Gwamnatin Afghanistan Sun Sake Кwace Garin Qala-e-Naw Daga Hannun Mayaƙan Taliban

Dakarun gwamnatin Afghanistan sun sami nasarar sake ƙwato garin Qala-e-Naw, babban birnin lardin Badghis a yau Alhamis ɗin nan bayan da mayaƙan Taliban suka mamaye da kuma ƙwace ikon garin.

ABNA24 : A wata sanarwa da Ma’aikatar tsaron ƙasar ta Afghanistan ta fitar ta ce dakarun gwamnatin sun sami nasarar fatattakan mayaƙan Taliban ɗin daga garin, duk da cewa har yanzu ana ɗan ɓarin wuta tsakanin ɓangarori biyu a wasu ‘yan wajaje a wajen birnin da ke kan iyaka da ƙasar Turkmenistan.

Sanarwar ta ƙara da cewa tuni aka tura da wasu ɗaruruwan sojoji sabon jinni yankin don ci gaba da tabbatar da tsaronsa da kuma ƙara fatattakan ‘yan Taliban ɗin.

Sanarwar Ma’aikatar tsaron ta ce an kashe mayaƙan Taliban 69 a yayin gumurzun bugu da ƙari kuma kan wani adadi mai yawa na makamai da aka ƙwato daga wajen mayaƙan.

A jiya Laraba ce dai mayaƙan na Taliban suka ƙwace wasu gine-ginen gwamnati ciki kuwa har da wasu helkwatoci na ‘yan sanda da ke birnin bayan sun kutsu cikin birnin a daidai lokaci da sojojin ƙasashen waje da Amurka take wa jagoranci suka bar ƙasar bayan kimanin shekaru 20 na mamaya.

Wasu rahotannin dai sun ce Taliban ɗin suna riƙe da ɗaruruwan gundumomi na ƙasar Afghanistan ɗin tun bayan da Amurka ta sanar da janyewarta daga Afghanistan ɗin duk kuwa da cewa dakarun gwamnatin da wasu dakaru na sa kai na al’umma suna ci gaba da tsayin daka wajen fatattakan ‘yan Taliban ɗin daga yankunan da suka ƙwace.

Gwamnati da kuma al’ummomin Afghanistan ɗin suna zargin Amurka da ƙawayenta da sanya su cikin irin wannan yanayi da suke ciki sakamakon mamayar da suka yi wa ƙasar wanda suka ce ba ta taɓuka musu komai ba in ban da ƙara sanya rayuwarsu cikin wahala da kuma barazana.

342/