8 Yuli 2021 - 13:17
An Bukaci Kasashen Afrika Su Kara Azama Kan Aikin Gona

Yayin da ake ci gaba da yaki da annobar COVID-19 gami da matsalolin sauyin yanayi, an bukaci kasashen Afrika su mayar da hankali wajen gina hukumar aikin gona ta zamani domin samun wadatar abinci.

ABNA24 : Da yake sanar da hakan, shugaban gamayyar shirin bunkasa aikin gona ba tare da gurbata muhalli ba na Afrika (AGRA), Hailemariam Desalegn, ya bayyana cewa, annobar COVID-19 ta tilasta a gaggauta daukar matakan bunkasa aikin noma wanda zai shafi kowace kasa da kowace nahiya da kuma dukkan al’umma.

Game da batun cutar COVID-19 da kalubalolin sauyin yanayi kuwa, tilas ne Afrika ta yi amfani da matasa, da mata, da maza, da yara da shugabannin siyasa, domin sauya tsarinta na samar da abinci, Hailemariam Desalegn ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da shirya taron kolin AGRF na wannan shekara wanda ake sa ran gudanarwa tsakanin ranar 6 zuwa 10 ga watan Satumba a Nairobi.

342/