7 Yuli 2021 - 14:11
Shugaban Ivory Coast, Ya Taya Zababben Shugaban Iran Murna

Shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Ouatara, ya taya zababben shugaban kasar Iran, Ebrahim Raïssi, murna kan nasara da ya samu ta lashe zaben shugabancin kasar ta Iran.

ABNA24 : Sakon na shugaba Ouatara na cewa’’ sahihin zaben da akayi maka a wannan mukami mai girma na shugabancin Iran, ina mai taya ka farin ciki da sunan gwamnati da al’ummar Ivory Coast, da kuma ni kai na’’

Ebrahim Raïssi, ya lashe zaben shugabancin kasar ta Iran, karo na 13 da da aka gudanar a ranar 18 ga watan Yuni da ya gabata, da kuri’u sama da miliyan 18, kuma tun lokacin ne ya ke ci gaba da samun sakonnin taya murna daga shugabannin kasashen duniya daban daban.

A cikin watan Agusta mai zuwa ne za’a rantsar da Ebrahim Raïssi, a matsayin sabon shugaban kasar ta Iran, inda zai maye gurbin shugaba Hassan Ruhani, wanda ke kan kammala wa’adin mulkinsa na biyu kuma na karshe.

342/