ABNA24 : Hukumonin Bamako dai sun bukaci hukumar ‘yan sanda ta kasa da kasa da kuma ‘yan sanda yaki da miyagun laifuka su cafke Karim Keita a duk inda ya ke, su kuma tiso keyarsa zuwa Bamako.
Tsohon dan majalisar dokoki, kana da ga hambararen shugaban kasar ta Mali, Karin Keita, ana zarginsa da hannu a batan wani dan jarida na kasar mai suna Birama Toure.
Karim Keita, dai ya jima yana musanta hannunsa a batan dan jaridan wanda ya yi batan dabo yau kusan shekaru biyar da suka gabata.
Kafofin yada labarai da dama daga Malin, sun ce Karin Keita, bai rasa masaniya game da batan dan jaridan dake wa jaridar binciken kwakwaf ta « Sphinx » aiki.
Karim Keita dai ya bar Mali ne tun bayan kifar da mulkin mahaifinsa, Ibrahim Bubakar Keita, a ranar 18 ga watan Agustan bara.
342/