Kamfanin dillancin labaran ABNA24 na kasar Iran ya nakalto Majid TakhtaRavanchi jakadan kasar Iran a majalisar dinkin duniya ya na fadar haka a gaban kwamitin tsaro na majalisar a birnin New York a jiya Litinin.
Jakadan ya yi kakkausar suka ga Antonio Gutteres kan rashin kawo batun killacewar da kawancen kasar Saudiya suke wa kasar Yemen, killacewar da ta haddasa talauci da yunwa ga yara, da kuma sanyasu cikin tashin hankali.
Daga karshe Jakadan ya ce killacewar ta tilasta masu zama yan gudun hijira, ta inda basa da damar samun karatu da kuma kiwon lafiyan da suka dace da su.
342/