ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Majid TakhtaRavanchi jakadan kasar Iran a majalisar dinkin duniya ya na fadar haka a gaban kwamitin tsaro na majalisar a birnin NewYork a jiya Litinin.
Jakadan ya yi kakkausar suka ga Antonio Gutteres kan rashin kawo batun killacewar da kawancen kasar Saudiya sukewa kasar Yemen, killacewar da ta haddasa talauci da yunwa ga yara, da kuma sanyasu cikin tashin hankali.
Daga karshe Jakadan ya ce killacewar ta tilasta masu zama yan gudun hijira, ta inda basa da damar samun karatu da kuma kiwon lafiyan da suka dace da su.
342/