27 Yuni 2021 - 13:41
​Iraki: An Cika Shekaru 7 Da Kafa Dakarun Hashd Al-shaabi

A yau ne ake gudanar da bukukuwan cikar shekaru 7 da kafa dakarun al’ummar kasar Iraki na Hashd al-shaabi.

ABNA24 : Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, a yau ne ake gudanar da bukukuwan cikar shekaru 7 da kafa dakarun al’ummar kasar Iraki na Hashd al-shaabi, bayan da shugaban addini na kasar Ayatollah Sayyid ali Sistani ya bayar da fatawar kafa rundunar sa kai ta al’umma domin fatattakar ‘yan Daesh, a alokacin da suke hankoron mamaye kasar.

Dakarun Hashd Al-sha’aabi sun gudanar da fareti a yau tare da nuna wasu daga cikin kayayyakinsu na yaki, kamar yadda kuma manyan kwamandojin rundunar gami da manyan jami’an tsaro da kuma jami’an gwamnati duk sun halarci wurin.

Firayi ministan kasar Iraki Mustafa Alkazimi na daga wadanda suka halarci taron fareti na dakarun Hashd Al-shaabi, inda kuma ya gabatar da jawabi a wurin, tare da tabbatar da cewa dakarun Hashd Al-sha’aabi ne suka taka muhimmiyar rawa wajen fatattakar ‘yan ta’addan Daesha daga Iraki, kuma har yanzu akwai sauran aiki a gabansu, domin kuwa ‘yan ta’addan suna nan, rauni ne kawai suka yi.

A cikin shekarar 2014 ne dubban mayakan ‘yan ta’adda daga kasashen duniya daban-daban suka shiga cikin kasar Irak ta kan iyakokin kasashen larabawa da suke makwabtaka da kasar, inda suka mamaye wasu yankuna a arewacin Iraki, amma bayan fatawar Ayatollah Sistani, an kafa rundunar Hashd Al-shaabi, wadda marigayi Kasim Sulaimani ya bayar ad gudunmawa wajen kafa ta, kuma su en suka kawo ragarza ‘yan ta’addan na Daesha Iraki.

342/