17 Yuni 2021 - 13:48
Kotun Ta Yi Watsi Da Buƙatar Netanyahu Na Jinkirta Shari’ar Rashawa Da Ake Masa

Rahotanni daga haramtacciyar ƙasar Isra’ila ta bayyana cewar alkalan kotun da ke shari’ar zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa tsohon firayi ministan Isra’ilan, Benjamin Netanyahu, sun ƙi amincewa da buƙatar Netanyahun na a jinkirta shari’ar da ake masan zuwa wani lokaci.

ABNA24 : Jaridar Yediot Ahranot ta Isra’ilan ce ta ba da wannan labarin inda ta ce lauyoyin Netanyahun ne suka buƙaci da a jinkirta shari’ar har sai bayan bukukuwan addinin yahudanci da za a gudanar a watan Satumba mai zuwa.

To sai jaridar ta ce alkalan kotun sun ƙi amincewa da wannan buƙatar inda suka ce shari’ar za a ci gaba da gudanar da ita kamar yadda aka tsara.

Tun a shekarar 2016 ne ‘yan sandan Isra’ilan suka fara gudanar da bincike kan zargin da ake wa tsohon firayi ministan kan rashawa da cin hanci da kuma almundahana. To sai dai kuma a shekara ta 2019 ne a hukumance aka gabatar da tuhumar da ake masa a gaban kotu kuma aka fara yi masa shari’a.

Ana ganin wannan buƙata ta lauyoyin a matsayin wani ƙoƙari ne na yin wasa da shari’ar da kuma jan lokaci sakamakon halin ƙasƙanci da shan kashi da Netanyahu yake fuskanta sakamakon cire shi da aka yi a matsayin firayi ministan bayan shekaru 12 yana mulki.

Idan dai aka same shi da laifi, to Netanyahun yana iya zama na wasu shekaru a gidan yari.

342/