16 Yuni 2021 - 13:22
Kafafen Watsa Labaran Кasashen Waje 226 Ne Za Su Watsa Zaɓen Iran Da Za’a Gudanar

Mataimakin ministan al’adu na ƙasar Iran kan lamurran da suka shafi kafafen watsa labarai, Muhammad Khodadi, ya bayyana cewar kimanin ‘yan jarida 500 ne da suka fito daga kafafen watsa labarai 226 na ƙasashen waje ne za su watsa labaran abubuwan da ke faruwa yayin zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar a Iran a ranar Juma’an nan mai zuwa 18, ga Yunin 2021.

Mr. Khodadi ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai inda ya ce wannan adadi na ‘yan rahoton suna wakiltar ƙasashe da kuma gwamnatoci 39 na duniya ne, sannan kuma za su shigo Iran ɗin ne bayan an gudanar musu da dukkanin bincike na lafiya musamman kan cutar nan ta Korona. Mataimakin ministan al’adun ya ƙara da cewa daga cikin ayyukan da waɗannan ‘yan jaridar za su gudanar har da halartar taron manema labarai da ministan cikin gida na Iran zai gudanar a yau laraba ɗin nan da kuma wani irin wannan taron da majalisar kula da kundin tsarin mulki na Iran ɗin za ta gudanar a gobe Alhamis haka nan kuma da kuma halartar bikin kaɗa kuri’ar Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a zaɓen shugaban ƙasar a ranar Juma’a. A jibi Juma’a 18 ga watan Yunin nan ake sa ran za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa karo na 13 a duk faɗin Iran don zaɓan sabon shugaban ƙasar.

342/