16 Yuni 2021 - 13:19
​Tarayyar Afrika Tana Bukatar A Shigar Da Manya-Manyan Kasashe 5 Don Warware Rikicin Madatsar Ruwa Ta Renaissance

Kungiyar tarayyar Afirka AU ta bukaci a shigar da manya-manyan kasashe 5 masu kujerun din din din a kwamitin tsaro na MDD a cikin rikicin madatsar ruwa ta Renaissance.

ABNA24 : Jaridar Sudan Tribune ta nakalto ministan ayyukan noman-rani na kasar Sudan Yasser Abbas ya na fadar haka. Ya kuma kara da cewa kungiyar ta AU ta bayyana wannan bukatar ce a wani ziyarar aiki wacce wata tawagar kungiyar, karkashin jagorancin babban sakataren kungiyar Moussa Faki ta kai birnin Karthum babban birnin kasar Sudan a ranar 14 ga watan yunin da muke ciki.

Yasser Abbas, ya kara da cewa gwamnatin kasar Sudan ba ta son wani abu in banda kasar Habasha ta yi amfani da dokokin kasa da kasa kan irin wadannan matsaloli, don samar da fahintar juna ta yadda za ta sarrafa madatsar ruwan, bisa ka’idojin da zasu gamsar da kasashe masu amfani da ruwan kogin Nilu.

Har’ila yau dangane da rikicin madatsar ruwan ta Renaissance ministan harkokin wajen kasar Masar Sameh Shukry ya kira taron gaggawa na ministocin harkokin waje a kungiyar kasashen larabawa a jiya Talata, inda ya bayyana masu halin da ake cikin dangane da rikicin madatsar ruwan.

342/