ABNA24 : Abbas Araghchi, ya ce zasu ci gaba da tattaunawa, muddin dai akai bukatar hakan.
A wata hira da tashar talabijin ta Press TV, Araghchi ya bayyana cewa sauran bangarorin da ke cikin yarjejeniyar dole ne su tabbatar wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran cewa abin da ya faru a baya (ficewar Amurka daga yarjejeniyar) ba za a sake maimaita shi ba a nan gaba.
Shugaban tawagar tattaunawar Iran din a Vienna ya ce: Don cimma wannan, muna bukatar tattaunawa da shawarwari da tuntuba, kuma za mu ci gaba da wadannan tattaunawar muddin hakan ya zama dole.
Araghchi ya ce "Har yanzu akwai batutuwan da ake bukatar a warware su."
A jiya Asabar ne, mataimakin Ministan Harkokin Waje kuma shugaban tawagar Iran, a tattaunawar ya isa Vienna babban birnin Austriya don ci gaba da tattaunawar neman farfado da yarjejeniyar nukiliyar ta Iran.
Wannan kuma shi ne kuma zagaye na shida a tattaunawar da ake.
Batun dagewa Iran takunkumi da dawowar Amurka a cikin yarjejeniyar, su ne manyan batutuwa da suka mamaye tattaunawar.
342/