14 Yuni 2021 - 09:35
Iran : Ruhani, Ya Taya Rasha Murnar Zagayowar Ranar Kasa

Shugaban kasar Iran Hassan Ruhani, ya taya kasra Rasha murnar zagayowar ranar kasa.

ABNA24 : A cikin wani sako da ya aike wa Shugaban Rasha Vladimir Putin, Shugaba Ruhani ya ce: "Ina mika sakon taya murna ta ranar tarayyar Rasha da gwamnati da kuma jama'ar kasar."

Ruhani ya kara da cewa: "Ina da yakinin cewa dangantakar abokantaka tsakanin Iran da tarayyar Rasha, wacce ke ci gaba a cikin 'yan shekarun nan, za ta ci gaba da fadada a dukkan fannoni da kuma muradun al'ummomin kasashen biyu fiye da da."

Kasashen Iran da Rasha, dai na dangantaka a fannoni da dama bayan kasancewarsu aminnan juna.

342/