ABNA24 : Shugaban Yankin ya sanar da kama mutumin da ya mari shugaban da kuma wani daban, kuma yanzu haka suna can suna amsa tambayoyi.
Samarin guda biyu duk ‘yan yankin na Drômois, masu shekaru 28, ba’a san su da aikata wani laifi ba, inji mai gabatar da kara na gwamnati a yankin Valence.
Tuni dai bangarori da dama da suka hada da ‘yan siyasa suka goyi bayan shugaban kasar, tare da yin tir da lamarin.
Ana saran shugaba Macron ya ziyarci yankunan kasar da dama a cikin watanni 2 masu zuwa domin ganawa da masu zabe gaba da gaba bayan kwashe sama da shekara guda ana fama da annobar korona.
342/