6 Yuni 2021 - 13:47
Wasu ‘Yan Mali, Sun Yi Maraba Da Matakin Faransa Na Dakatar Da Ayyukan Hadin Gwiwa Sojojin Kasar

A Mali, wasu ‘yan kasar sun ce Allah raka taki gona, game da matakin kasar Faransa, na dakatar da ayyukan hadin gwiwa da sojojin kasar.

ABNA24 : A jiya ne dai daruruwan magoya bayan yan adawar Mali da ake kira M5 suka gudanar da zanga zanga a birnin Bamako, yayin da gamayar na M5, ya cika shekara guda da kafuwa.

Tuni dai a malin, aka fara hasashen cewa za’a nada Choguel Maïga, jigo a jam’iyyun ‘yan adawan a matsayin fira ministan kasar.

Idan dai ana tune zanga zangar ‘yan adawan ta M5, ita ce ta yi silan sojoji suka kifar da mulkin tsohin shugaban kasar IBK.

Kayo yanzu dai Faransa ta bayyana dakatar da ayyukan hadin gwiwa tsakanin dakarunta da na kasar ta Mali, sakamakon juyin mulkin da sojojin kasar suka sake yi karo na biyu cikin watani 9.

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta ce matakin dakatar da ayyukan hadin gwiwar samar da tsaron zai cigaba da wanzuwa har zuwa lokacin da za a samu tabbaci daga sojojin na Mali sun mika wa farar hula mulki.

342/