ABNA24 : Jaridar Egypt daily ta bayyana cewa a taron na jiya da yau Talata dai, bangarorin biyu zasu tabo batutuwa wadanda suaka hada da, yan kasashen biyu da suke zaune a dayar kasar, kai kawon kayaki da mutane tsakanin kasashen biyu, tsaro da kuma da kamun kifi a cikin tekun medeteranian.
Egypt daily ta kara da cewa a halin yanzu kamfanin jiragen sama na kasar Masar wato Egypt Air ta aike da tawaga zuwa kasar Libya don bincike da gano yiyuwar fara zirga-zirgan jiragen sama tsakanin kasashen biyu.
Tawagar zata binciki yiyuwar saukar jiragen sama na Egypt Air a biranen Tripoli babban birnin kasar, da Misrata da kuma Mitigan. Idan har hakan zai yu akwai shirin zirga-zirgan jiragen Egypt Air har sau 35 a ko wani mako zuwa kasar ta Libya.
342/