2 Yuni 2021 - 13:23
​Akalla Mutane 10 Ne Suka Rasa Rayukansu A Tashe-Tashen Boma-Bomai A Birnin Kabul

Boma-bomai guda 3 ne suka tashi a birnin Kabul babban birnin kasar Afganistan inda suka yi sanadiyyar kashe mutane akalla 10.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa boma-bomai guda biyu na farko sun tashi ne a cikin wasu motoci a wata unguwa daga yammacin birnin Kabul a jiya Talata da yamma, a yayinda na 3 kuma ya tashi a wata cibiyar bada wutan lantarki na birnin wanda ya jefashi cikin duhu.

Kakakin ma’aikatar cikin gida na kasar Hamid Roshan ya ce ‘yan sanda sun killace yankunan da abin ya faru sun kuma fara bincike don gano musabbabin tashin bama-boman.

Ana zargin kungiyar Alqaed da kuma Taliban da hannu wajen kissan mutane a birnin na Kabul. Musamman a dai-dai lokacinda Amurka ta fara jenye sojojinta daga kasar.

342/