ABNA24 : Jaridar Egypt Today ta nakalto Assisi yana fadar haka a jiya Talata, bayan da ya karmi rahoton babban jami’an ayyukan ‘yansandan ciki na kasar Abbas Kamel wanda ya kai ziyara zuwa yankin na Gaza na ranar litinin.
Assisi ya ce za’a fara ayyukan sake ginin yankin Gaza ne bayan bukatar da ya samu na yin haka daga shugaban gwamnatin cin gashin kan Falasdinawan Mahmood Abbas, sannan ya ce a yi aikin ne karkashin kula da manya manyan kasashe da kungiyoyi a duniya, wadanda suka hada da Amurka da kuma MDD. Ya zuwa yanzu dai an samu dalar Amurka miliyon 500 don sake gidan yankin na Gaza bayan rushe-rushen da jiragen yakin HKI suka yi a yaki tsakaninta da masu gwagwarmaya a yankin.
342/