ABNA24 : Cibiyar da take kula da wadanda su ka bace a lokacin yakin Bosnia ta sanar da cewa; An gano kabarin ne a kauyen Dobro Polje a kudancin garin Kalinovik.
Tun bayan kare yakin Bosnia zuwa yanzu an gano manyan kabaruka da su ka haura 550 dukkaninsu na musulmin da aka yi wa kisan kiyashi a karkashin rusasshiyar Yogoslavia.
342/