29 Mayu 2021 - 14:18
​Mali:Wata Kotu Ta Tabbatar Da Assimi Goita A Matsayin Shugaban Riko Na Kasa

Assimi Goita shugaban juyin mulkin da aka yi a kasar Mali a cikin makon da ya gabata ya zama shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar har zuwa karshe aikin mika mulki ga fararen hula.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa Goita shi ne mataimakin shugaban kasar da aka tilasta masa sauka bayan wani sabanin da ya shiga tsakaninsu.

Labarin ya kara da cewa Goita ne ya jagorancin dukkan juye-juyen mulkin da aka yi a kasar ta Malai a cikin watanni da suka gabata a kasar.

Goita dan shekara 38 a duniya shi ne ya jagoranci kama shugaban kasa da Firai ministansa bayan wani garin bawul da suka yi wanda ya sauke ministoci biyu daga mukamansu. A ranar Lahadi mai zuwa ne ake saran shwagabannin kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka zasu gudanar da taro don tattauna wannan matun.

342/