ABNA24 : Ayatullah Sayyid Ali Imam Khamnei ya kara da cewa; “ Zukatanmu sun kasance a tare da ku a filin daga, kuma mun rika yi muku addu’a domin samun nasara.”
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya ambato cewa; Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Imam Khamnei ya bayana haka ne a cikin jawabin wasikun da shugabannin kungiyoyin gwagwarmaya biyu Isma’ila Haniyya na Hamas, da Ziyad Nakhala na Jihadul-Islami, su ka aiko masa a baya.
Jagoran Juyin Juya halin musuluncin na Iran ya kuma bayyana cewa; Da yardar Allah al’ummar Palasdinu za su ga nasara ta karshe ba da jimawa ba.
342/