ABNA24 : Kakakin hukumar NEBE Solyana Shimelis, ya ce an tsara sabon jadawalin zaben ne bayan la’akari da bukatar kammalawa da sufurin takardun zabe zuwa mazabun dake fadin kasar.
A baya, an sanya 5 ga watan Yuni a matsayin ranar babban zaben karo na 6, amma na wucin gadi.
A cewar kakakin, baya ga zabukan ‘yan majalisun dokoki da na jihohi, za a gudanar da zaben raba gardama kan yuwuwar kirkirar sabuwar jiha ta 11 a ranar 21 ga watan na Yuni.
Fiye da al’ummar Habasha miliyan 31.7, ne suka yi rejista domin kada kuri’a a babban zaben karo na 6 dake tafe.
342/