21 Mayu 2021 - 13:38
Rundunar Sojin Nijeriya Na Bincike Kan Labarin Mutuwar Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau

Rundunar sojan Nijeriya ta ce tana gudanar da bincike game da wasu labarai da suke cewa an kashe shugaban ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau sakamakon wani rikici da ya shiga tsakaninsa da ‘yan ƙungiyar ISWAP da ta ɓālle daga Boko Haram ɗin.

ABNA24 : Rahotanni daga Nijeriya ɗin sun ce mai magana da yawun rundunar sojin ƙasar, Birgediya Mohammed Yerima ne ya sanar da hakan inda ya ce ba za su ce komai ma dangane da wannan labarin har sai sun gama binciken da suke yi kan lamarin.

A jiya ne dai aka ruwaito labarin mutuwar Abubakar Shekau ɗin bayan ‘yan ƙungiyar ISWAP ɗin sun kama shi a maɓoyarsa da ke dajin nan na Sambisa da ke jihar Borno biyo bayan gumurzu tsakanin ƙungiyoyin biyu da kuma nasarar da ‘yan ISWAP ɗin suka samu a kan dakarun Abubakar Shekau ɗin.

Labarin dai ya ce shi Shekau ɗin ne ya kashe kansa lokacin da ya tayar da bama-baman da yayi jigida da su bayan da ‘yan ISWAP ɗin suka kama shi da kuma ci gaba da tattaunawa da shi kan ya miƙa wuya da kuma yi musu mubaya’a.

342/