19 Mayu 2021 - 14:00
​Iran:Ana Ci Gaba Da Shirye Shiryen Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A cikin Watan Yuni Mai Zuwa

A ranar 18 ga watan yuni mai zuwa ne za’a gudanar da zaben shugaban kasa a nan Iran. Tuni dai an yiwa mutane kimani 600 wadanda suke neman wannan kujerar rijista daga ranar 11 ga watan Mayu da muke ciki har zuwa na kwanaki 5.

ABNA24 : A halin yanzu dai mataki na gaba shi ne tantance wadanda suka yi rijsitar sunayensu don fitar da wadanda suka fi cancantar tsayawa takarar neman kujerar, wadanda kuma za’a bayyana sunayensu a ranar 26 ga watan Mayu da muke ciki.

Sannan daga ranar 28 ga watan Mayu zuwa 16 ga watan Yune ne ake saran yan takarar da suka tsallaka tantancewar zasu fara yakin neman kuri’un mutane. Sannan kwanaki biyu bayan hawa, wato ranar 18 ga watan Yuni za’a gudanar zaben shugaban kasa da wasu zabubbuka a duk fadin kasar.

Fiye da mutane miliyon 57 ne suka cancanci kada kuri’a a zaben daga cikin mutane fiye da miliyon 80 a kasar.

Sannan idan ba wanda ya sami fiye da kashi 50% na yawan kuri’un da aka kada za’a gudanar da zabe zagaye na biyu a ranar 25 ga watan na Yuni tsakanin ‘yan takara biyu wadanda suka fi kowa yawan kuri’u a zagaye na farko.

Daga karshe, idan an zabi shugaban kasa, jagoran juyin juya halin musulunci zai tabbatar da wanda aka zaban, ya kuma bashi takardar shaidar hakan daga baya.

342/