13 Mayu 2021 - 19:04
IRGC: Za Mu Kara Bai Wa Palasdinawa Taimako Fiye Da Kowane Lokaci

Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran sun yi tir da laifukan da HKi take tafkawa ta hanyar kutsen da ‘yan sahayoniya su ke yi a cikin masallacin Kudus da kuma yankin Gaza, tare da jaddada ci gaba da bayar da taimako ga gwagwarmayar Palasdinawa fiye da kowane lokaci a baya.

ABNA24 : A jiya Laraba ne dai dakarun kare juyin musuluncin na Iran su ka fitar da wata sanarwa da a ciki su ka bayyana cewa; Boren da Palasdinawa su ka yi a cikin watan Ramadan da kuma yadda ‘yan gwgawarmaya su ke fadada yankunan da suke kai wa hari a HKI da kuma yadda kananan yara da mata masu yawa su ka yi shahada, ya fusata al’ummar musulmi da kuma duk masu son ‘yanci a duniya.

Bugu da kari sanarwar ta dakarun kare juyin musulunci ta ci gaba da cewa; Abinda yake faruwa ya sake bayyana hakikanin tsarin sahayoniya ‘yan mamaya da kwace da kuma masu ba shi kariya.

342/