ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Abbas Araqchi ya na fadar haka a yau Laraba a shafinsa na Twitter.
Ya kuma kara da cewa matukar an dauke wa kasar Iran takunkuman tattalin arzikin kafin ranar 21 ga watan Mayun da muke ciki, kamar yadda hukumar ta yiwa kasar alkawari, Iran zata bude kofarta ga hukumar ba tare da wani bata lokacin ba.
Kafin haka dai a ranar 23 ga watan Fabrairun da ya gabata ne kasar Iran ta dakatar da bada hadin kai ga hukumar ta IAEA saboda dokar da majalisar dokokin kasar ta kafa, na dakatar da hadin kan, sai zuwa lokacinda Amurka za ta daukewa kasar takunkuman tattalin arzikin.
342/